Daga karshe: Buratai ya bayyana lokacin da ta'addanci zai kare a Najeriya

Kasa da sa'o'i 24 da bayyana kisan wasu sojoji a wani bangare na kasar, shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, ya je fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Abuja a ranar Litinin.

Buratai ya je bayyanawa shugaban kasar inda aka kwana a wurin yaki da rashin tsaro. A yayin ganawa da manema labarai bayan taron, ya ce domin shawo kan wannan matsalar, dole ne dukkan 'yan Najeriya su hada kai wurin yaki da ta'addanci.

Ya ce duk da ta'addanci sabon abu ne a kasar nan, rashin tsaro ya dade amma abu mafi muhimmanci shine yadda za a shawo kan shi. Kamar yadda yace, duk da cewar akwai kalubale wajen shawo kan matsalar, hakan ba yana nufin masu kula da tsaron basa kokarin bane.

Buratai ya ce: "A kan cewa ko ta'addanci da al'amuran 'yan bindiga zai zo karshe, ina tunanin hakan ya danganta ne da yadda 'yan Najeriya ke so. Ina tabbatar mana zai zo karshe idan kowa ya hada kai saboda 'yan bindigar nan ba daga kasashen ketare suke ba.

"Wadannan yan ta'adda, kaso 99 cikin 100 'yan Najeriya ne. Masu garkuwa da mutanen duk 'yan Najeriya ne. "Don haka, ba dakarun soji ko wasu cibiyoyin tsaro bane za su kawo karshen rashin tsaro ba. Idan abu ya cabe ne ake kiranmu amma hakkin kowa ne tsaron kasa.

"Wasu daga cikin rashin tsaron sun dade sosai kuma duk ya danganta ne da abunda ake yi domin magancesu a wani kayadadden lokaci. Kokarinku ne zai kayyade lokacin da rashin tsaro zai kare a kasar.

"Ba tun yanzu muke fama da fashi da makami ba. Tuntuni akwai shi a kasar nan tun kafin haihuwarmu. Garkuwa da mutane kuwa ya dade fiye da tarihin kasar nan amma lokaci ne yasa ya kara yawaita.

"Ta'addanci za mu iya cewa shine sabo. Mun fara fuskantar shi amma muna shawo kanshi kamar sauran matsalolin tsaro. "An yi lokacin Maitatsine. Tuni kuwa yayi kaura tun a lokacin, don haka ta'addanci zai zo karshe amma duk ya danganta da yadda muka shawo kan shi da dakile yaduwar sa.

"Ina tabbatar muku da cewa babu dadewa za mu kawo karshen komai kuma tsaron kasar nan zai inganta a kowanne sashen kasar." Buratai ya tabbatar da cewa ya je fadar shugaban kasar ne don sanar da shi nasarorin da aka samu a cikin aikin da aka bashi.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN