Ganduje ya saki fursunoni 293 a Kano

Rahotun Legit Hausa

A jiya ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya saki fursunoni 293 da ke zaman cin sarka a wani mataki na gyara hali cikin gidajen kaso da ke fadin jihar.
An saki fursunonin masu kananan laifuka bisa ga umarnin da Gwamnatin Tarayya ta yi wa gwamnatocin jihohi na rage cunkoso a gidajen gyara hali da ke fadin kasar biyo bayan barkewara annobar cutar korona.
Kakakin Hukumar Gidajen Yari ta kasa reshen jihar Kano, DSC Musbahu Lawan Nassarawa, shi ne ba da tabbas a kan wannan lamari na 'yantar da fursunoni kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
DSC Lawan ya shaidawa manema labarai cewa, bayan biyan tara ta kimanin naira miliyan 12 da gwamnan ya yi, ya kuma ba wa kowane daya daga cikin fursunonin da suka shaki iskar 'yanci naira 5,000 kudin komawa gida.

A daya daga cikin gidajen gyara halin da Gwamna Ganduje ya kai ziyara, ya umarci fursunonin da su kasance nagari kuma su yi amfani da wannan dama da aka basu wajen neman na-kai da zai hana su aikata miyagun laifuka.
Kwanturola na Hukumar Gidajen Yari reshen jiharKano, Mahaji Ahmed Abdullahi, ya yaba da matakan hana yaduwar cutar korona a dukkan gidajen gyara hali na kasa da Kwanturolan Hukumar na kasa, Jafaru Ahmed ya shimfida.
Ya kuma yi godiya tare da yabawa Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje dangane da fadi-tashin da ya ke yi na goyon baya da hadin kai da yake ba wa ma'aikata da fursunoni.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN