Ban san saduwa da miji wajen kwanciya hakkin aure bane, inji Amarya da ta kashe Ango

Rahotun Legit

Wata matar aure mai shekaru 18 mai suna Salma Hassan da ke karamar hukumar Itas Gadau ta jihar Bauchi, ta shiga hannun 'yan sandan jihar sakamakon zarginta da ake da sokawa mijinta wuka.

Ana zargin Salma ta kashe mijinta mai suna Mohammed Mustapha ne a kan auratayya. Salma, yayin da ta shiga hannun 'yan sandan a hedkwata da ke Bauchi, babban birnin jihar a ranar Alhamis, ta ce ta soka wa mijinta wuka ne saboda ya takurata dole sai ya kwanta da ita a daren.

Kamar yadda ta bayyana a hedkwatar 'yan sandan, ta ce "Ban so kashe mijina ba, tsautsayi ne. Na soka mishi wuka a kirji ne saboda ya takura ni dole sai ya kwanta dani. Na zata iskanci ne jima'i, shiyasa na ki amince wa. "Na yi dana-sanin kashe mijina.

Na so amfani da wukar ne don tsorata shi. Ban san cewa hakan za ta faru ba," ta kara da cewa. Salma wacce ta bayyana cewa tana matukar son mijinta, ta ce ta fusata ne don ya ki daina abinda yake nufin yi da ita.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Philip Maku, a yayin zantawa da manema labarai yace Salma ta yi aika-aikar ne a ranar 24 ga watan Afirilun 2020.

Ya ce wani mutum mai suna Haruna Musa ne ya kai rahoton zuwa ofishin 'yan sandan da ke karamar hukumar Itas-Gadau inda daga bisani suka damke ta. Maku yace Mustapha ya ji miyagun raunika kuma an hanzarta kai shi asibiti amma sai aka tabbatar da cewa ya mutu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN