Shari'a za ta yi iyaka tsakanin Arewa24 da hukumar tace fina-finai

Rahotun Legit Hausa

Bayan dakatar da haska shirin Kwana Casa'in da Gidan Badamasi da hukumar tace fina-finai ta jihar Kano tayi, alamomi na bayyana cewa gidan talabijin din Arewa24 ba zai bi hakan ba.

A jiya ne dai Legit.ng ta ruwaito cewa, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, a karkashin shugabancin Isma'il Na'Abba Afakalla ta ba gidan talabijin mai zaman kanshi na Arewa 24 umarnin dakatar da haska fina-finan Kwana Casa'in da Gidan Badamasi.

Ta basu wa'adin sa'o'i 48 ne don tabbatar da an dena haska su saboda sun taka dokar jihar Kano. Kamar yadda wani sashi na takardar da hukumar ta aika wa gidan talabijin din ta bayyana, ta ce ta dauka wannan matakin ne saboda wani sashi na fim din kwana casa'in din ya saba wa al'adar jama'ar jihar Kano.

Akwai wani sashi da aka nuna a shirin makon da ya gabata, inda aka nuna wani mutum ya rungumi wata a cikin wani kantin sayar da kaya na Sahad Stores da ke Kano. Kamar yadda jaridar Daily Trust Aminiya ta ruwaito, hukumar ta ce tana da alhakin dubawa tare da tantance duk wani fim da aka shirya da Hausa.

A don haka ne take bukatar cewa duk wani fim din na kwana casa'in da za a kara haskawa, sai ta tace. amar yadda masu sani suke zargi, an dakatar da shirye-shiryen ne saboda suna da alaka da siyasa. Masani kuma mai nazari a fannin fina-finan Hausa, Muhsin Ibrahim, wanda ke koyarwa a kasar Jamus ya ce ba wannan ne karo na farko da ake tuhumar shirye-shiryen da karya doka ba.

Ya ce akwai fitowar da aka cudanya mata da maza a shirin Dadin Kowa, amma hukumar ba tace komai ba saboda shirin bai shafi siyasa kai tsaye ba. Ya kara da cewa, ya kamata hukumar tace fina-finai ta bi hanyar lalama ne a lamarin, ballantana idan Arewa24 ta ci gaba da nuna shirye-shiryen. Koda kuwa kotu aka je, akwai yuwuwar Arewa24 tayi nasara kuma a ja musu iyaka da hukumar tace fina-finan.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN