Yadda direba ya ci amanar ubangidansa ya yi wa diyarsa fyade ta dau ciki

Rashin hakuri, kwadayi da cin amana ya jefa wani direba mai suna Mr. Friday cikin tashin hankali sakamakon cin amanar uban gidansa. Mr Friday wanda ke daukan yayan ubangidansa zuwa makaranta dai ya yi amfani da karfi kuma ya yi wa wata diyar ubangidansa yar shekara 13 fyade sakamakon haka yarinyar ta dau ciki.

Majiyarmu ta ce lamarin ya faru ne bayan wata rana direba Mr. Friday ya zo domin ya dauki yaran zuwa makaranta, kasancewa an yarda da shi har ma yana shiga cikin gidansu, kuma bayan kasancewa direba, abokin mai gidan ne wanda babban Manaja ne a wani Kamfanin man fetur a Sapele na jihar Delta. Bayan Friday ya shiga gidan ne sai ya tarar yarinyar tana fitowa daga dakin wanka, gogan naka ya rude kuma fa ya rungumeta ya tausheta ya yi mata fyade.

Bayan ya aikata wannan aikin ne daga bisani kuma ciki ya shiga bayan wani lokaci, sakamakon haka ne iyayen yarinyar suka kore shi daga aikinsa kuma suka mika shi ga yansanda domin ya fuskanci tuhuma.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN