Mutane biyar sun warke daga cutar coronavirus a Najeriya,an sallamesu sun koma gida

Rahotun Legit Hausa

A ranar Litin ne gwamnatin jihar Legas ta sallam wasu mutane biyar daga cibiyar killacewa da ke asibitin cututtuka masu yaduwa a unguwar Yaba bayan an tabbatar da cewa yanzu basa dauke da kwayar cutar coronavirus.

Ya zuwa yanzu an sallami jimillar mutane 8 kenan daga cibiyar. Mutanen da aka sallama suna cikin koshin lafiya, babu alamar gajiya ko damuwa a tare da su, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito. Duk da mutanen da aka sallama sun zabi a sakaya sunayensu, sun bayyana jin dadi da gamsuwarsu a kan irin kulawar da suka samu a cibiyar.

A yayin da suke mika godiya ga gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, bisa gudunmawa da kokarinsa na ganin an shawo kan annobbar cutar covid-19, mutanen sun nemi hukuma ta kara kyautatawa ma'aikatan cibiyar.

Da yake magana da manema labarai, daya daga cikin wadanda aka sallama ya ce, "an kawoni wannan cibiya a ranar 15 ga wata bayan sakamakon gwajin da aka yi min ya nuna cewa ina dauke da kwayar cutar.

 "Da farko na fuskanci kalubale amma daga bisani komai ya daidaita. Ma'aikatan cibiyar sun yi matukar kokari wajen bamu kulawa, ni da abokaina shaida ne a kan hakan." Ya bawa jama'a kwarin gwuiwar cewar kar su wani firgita saboda kwayar cutar coronavirus saboda ana warkewa, alamar da ke nuna cewa za a samu galaba a kan kwayar cutar.

A ranar Lahadi ne hukumar kasar Saudi Arabia ta sanar da cewa wasu mutane 66 da suka kamu da kwayar cutar coronavirus sun warke. Sanarwar na kunshe ne a cikin sakon da babbar jaridar kasar Saudiyya da ake wallafa wa cikin harshen turanci; 'Saudi Gazette' ta fitar ranar Lahadi. Akwai kimanin mutum 96 da aka tabbatar da cewa sun kamu da kwayar cutar coronavirus a kasar Saudiyya tare da asarar rayukan mutane 8.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN