Duba dalili da ya sa FRSC ke sayar da littafin ka'idodin tuki da dokokin hanya

Sakamakon wani bincike da Mujallar ISYAKU.COM ya gudanar a jihar Kebbi, ya nuna cewa littafin dokokin hanya da hukumar kiyaye hadurra ta kasa ke sayarwa a bisa doka yake.

Littafin wanda ake kira Nigerian high way code, user handbook ana sayarwa ne a kan kayyadadden farashi domin masu amfani da ababen hawa su san dokoki da ka'idodin tuki,  da amfani da ababen hawa a titunan Najeriya.

Sayar da wannan littafi da hukumar kiyaye hadurra ke yi a kan naira dubu daya (N1000) ya jawo kace-nace a shafukan sada zumunta, musamman a garin Birnin kebbi.

Sai dai bincike da muka gudanar, ya nuna cewa ana karbar kudin ne domin zama farashin littafin wanda bugawa ne aka yi kuma ana biyan kudi wajen bugawa.

Binciken ya fayyace cewa littafin, mallakin hukumar ce da take wallafawa, amma tara da ake yi ma wadanda suka aikata laifin tuki, hakkin gwamnatin tarayya ne saboda ana kai kudin taran ne kai tsaye a asusun bai daya na gwamnatin tarayya.

Wata majiya mai kwari , ta shaida mana cewa, "Ba wai sai an kama mutum da lifin tuki ake sa ya saye littafin ba, hatta wasu ,utane sukan zo su saye wannan littafi domin amfanin kansu".

Majiyar ta kara da cewa " Akan sayar wa mai laifi da littafin ne, saboda ya san ka'idodin tuki a titi domin kada ya kara maimaita wannan laifi. Ya ce, FRSC tana da hakkin kai mai laifi Kotu, amma ta gwammace ta yi wa mai laifi tara, domin ya biya, ya kuma kiyaye gaba, shi ya sa ake saidawa mai laifin tuki wannan littafi".

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  

Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN