Coronavirus: Duba abin da wata kungiya ta yi wa Malamai da Almajirai a jihar Kebbi

Kungiyar kare yanci da fafutukan kare 'yancin arewa Movement for Northern Nigeria Liberty, ta kai ziyarar fadakarwa ga Makarantar Allo na Almajirai, domin fadakarwa kan ababe da ya kamata Malamai da Almajirai su yi domin kaucewa kamuwa, da yaduwar cutar coronavirus.

Kungiyar ta ziyarci makarantar Malam Katune a unguwar Rafin Atiku, inda shugabanta na jihar Kebbi Capt. Abubakar Musa Sambawa (Soja), ya yi bayani yadda ya kamata Malamai da Almajirai su yi domin ganin an dakile yaduwar cutar.


Sakataren kungiyar ta kasa, Mal. Adamu Attahiru, ya kara fadada bayanin ga Malamai da Almajirai kan ababe da ya kamata su sani dangane da cutar. Daga bisani Mal. Abubakar Labaran Arab, ya zuba wa Malamai da Almajirai man tsabtace hannaye (Sanitizers) domin manuniya da kariya ga cutar.

Hakazalika, Mal. Lukman Hamidu Yauri , Malama Hannatu Abdulkadir, tare da sauran mambobin kungiyar, sun bi sahu wajen zuba wa Almajirai man tsabtace hannu (Sanitizers)

Malam Katune, ya godewa yan kungiyar, bisa ziyara da kulawa da suka nuna wa Makarantarsa da dalibanta, ya kuma sha alwashin zai cin gaba da fahimtar da dalibansa kan ababe da kungiyar ta sanar da su.

Kungiyar kare 'yanci da fafutukar kare 'yancin arewa (Movement for Northern Nigerian Liberty), tana da mazaunin dindindim a birnin Abujan Najeriya, inda take gudanar da ayyukanta ta ressanta da ke jihohin arewa, karkashin shugabancin shugabannin kungiyar na jihohi, wadanda ke karbar umarni daga shugaban uwar kungiyar ta kasa da ke Abuja.

Rahotun Isyaku Garba Zuru @isyakulabari

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Latsa nan ka zabi masoyiyarka daga jerin 'yan mata da ke neman aure ko soyayya  

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN