Type Here to Get Search Results !

Tap di jan: Yadda wata mata ta cije al'aurar mijinta har ya gundule, karanta dalili

An garzaya zuwa Asibiti da wani mutum mai suna Sibangilizwe Ngamula, bayan matarsa ta cije kan al'aurarsa sakamakon haka kan kaciyar al'aurarsa ya gundule a kasar Zimbabwe.

Majiyar isyaku.com ta ce an sha samun matsala tsakanin Sibangilizwe da matarsa bisa zargin neman maza, wanda matarsa ta sha musantawa, sakamakon haka ake yawan samun tashin hankali a gidan.

Bayanai sun nuna cewa sakamakon haka, matarsa ta kwashe kayanta ta tafi gidansu har ta yi mako biyu.

Bayan ta dawo ne kuma, sai rikici ya sake kaurewa tsakanin ma'auratan, sakamakon bacewar makullin daki, wannan lamari ya sa matar Sibangilizwe ta dunkule hannunta ta kai wa mijinta duka a fuska,  ta kuma cakume golayensa ta murde su har ya fadi, daga bisani kuma ta kama  al'aurarsa ta gatsa masa cizo mai tsanani da hakoranta har kan al'aurar ya cire.

Saidai an garzaya da Sibangilizwe zuwa Asibiti inda yake jinya, amma wata majiya a Asibitin ta ce Sibangilizwe zai iya ci gaba da jima'i duk da yake kan al'aurarsa ya cire kuma wasu jijiyoyin al'aurar sun tabu.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari

Top Post Ad

Below Post Ad

Shiga group dinmu na WhatsApp domin samun labaran mu kai tsaye LATSA NAN
Domin zama Wakilin mu a garin ku LATSA NAN
Domin aiko Sako/Labari/Korafi LATSA NAN
Domin samun labaran mu a Facebook LATSA NAN
Domin samun labaranmu a Twitter LATSA NAN