Asirin fasto ya tonu, bayan wani mutumi ya bayyana yadda ya kama shi yana kwanciya da matarshi da kuma 'yarshi

Rahotun Legit Hausa
Wani mutum dan asalin Najeriya mai zama a kasar Amurka ya fallasa faston da yake lalata da matar shi da diyar shi amma kuma yana kokarin jawo hankulan mutane a kan illar hakan, kamar yadda jaridar Gistmania ta ruwaito.
A daya daga cikin tsokacin da aka yi bayan wallafa bidiyon, ma’abocin amfani da kafar sada zumuntar ta zamani ya ce: “Babu shakka littafin bibul yayi gaskiya. Yace daga coci za a fara hisab... Abin haushin shine yadda mutane ke zuwa coci duk ranar Lahadi tare da ikirarin cewa sun fi wadanda basu zuwa… Da yawa daga cikin masu addinin garagajiya sun fi mu,”
Ba wannan karon bane dai aka fara kama fastoci na kwanciya da matan aure ko ‘yan mata ba. A kwanakin baya wata mata tayi korafin yadda fastonsu ke zuwa har cikin gida a kan gadon mijinta yake kwanciya da ita.
Da farko wani ciwo ne ya sameta wanda ya ja suka garzaya wajenshi neman magani tare da mijinta. Bayan ta dau kwanaki tana amfani da maganin, sai ya kare kuma ciwo ya dawo. Tuni suka kara komawa wajen faston wanda ya shawarcesu da su koma gida zai dinga zuwa da kanshi yana mata magani.
Daga nan ne fa kofa ta bude don kuwa yana zuwa har cikin gidanta koda mijin na nan sai su kulle kofa. Duk zuwanshi kuwa yana samun damar kwancya da ita a kan gadon mijinta tare da morarta yadda ya so.
Tana son sanar da mijinta mummunan lamarin amma ba ta san yadda zai dauka ba.
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN