An tsinci gawar saurayi da budurwa a dakin janerato a unguwar Badawa a Kano

Rahotun Legit Hausa

Wani mutum mai suna Auwallu Abdullahi mai shekaru 25 da budurwasa mai shekaru 19 an tsinci gawarsu a dakin janareto a Unguwar Gaya da ke yankin Badawa a cikin birnin Kano. 

Ana zargin masoyan biyu sun mutu ne sakamakon hayakin janareton bayan sun kulle kansu a dakin Janareton na dogon lokaci. Lamarin ya faru ne wajen karfe 9 na dare a ranar Laraba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. 

Majiya ta sanar da jaridar Daily Trust cewa wata matar aure ce ta gano gawawwakin a dakin Janareton da ke gidan. An ce matar ta hanzarta sanar wa 'yan sanda wadanda suka hanzarta mika masoyan asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano inda aka tabbatar da mutuwarsu.

A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce hukumar sun samu labarin ne wajen karfe 9:30 na daren Laraba. 

Ya ce jami'an sun hanzarta zuwa wajen inda suka kwashesu zuwa asibitin kwararru na Murtala. A nan ne aka tabbatar da mutuwar dukkansu biyun. Ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Habu A.
Sani, ya bada umarnin tsananta bincike don gano yadda wannan abin mamakin ya faru. 

Wata majiya wacce ba mai karfi ba ta tabbatar da cewa Auwallu Abdullahi da budurwarsa na kokarin yin aure ne kafin aukuwar mummunan lamarin. 

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari

Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN