An sace motar daukan gawa dauke da gawar wata mata

Rahotun Legit Hausa

Hukumomi a jihar Los Angeles, kasar Amurka, sun fara gudanar da bincike a kan yadda aka sace wata motar daukan gawa da aka sace dauke da gawar wata mata a ciki. An sace Motar, kirar 'Lincoln Navigator ' mai bakin fenti, a gaban Cocin St. Anthony da ke California yayin da direbanta ya tsaya domin sauke wata gawar.

Daily Nation ta rawaito cewa direban motar ya nemi motar ya rasa bayan ya fito daga Cocin St. Anthony, inda ya sauke wata gawa.

A wani rahoto da ABC ta wallafa a ranar da abin ya faru (26 ga watan Fabrairu), hukumomi sun roki barawon motar ya daure ya dawo da gawar matar da ke cikin motar idan ma ba zai dawo da motar ba"Haba!

Duk da cewa barawo ya saba aikata laifi, ya kamata wannan barawo ya yi abin kirki sau daya a rayuwarsa; ya dawo da gawar da ke cikin akwatin gawa a cikin motar," a wata sanarwa da jami'in dan sandan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Tuwita.

Sai dai, hukumomin basu bayyana sunan wanda ake zargi da sace motar ko sunan matar da gawarta ke cikin motar ba. Mahukuntan Cocin sun bayyana cewa sace motar da gawar matar da ke cikin motar da aka sace su da alaka da harkokin Cocin.

DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/CSYKJgAmLEF4s1dle0Ug6J

Duba kasuwanci da za ka sami ribar kaso 200 a rana daya kacal. LATSA NAN ka bincika  
Saratu ta warke cutar olsa (ulcer) da ta yi fama da shi, karanta ababe da ta hada ta sha 

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN