Bayan haka, wani mutum mai suna Bamidele Olanrewaju, a jihar Ogun ya hallaka matarsa, Adenike, a ranar Lahadi, 19 ga Junairu, 2020 a gidansu dake kauyen Bisodun, karamar hukumar Obafemi-Owode, jihar Ogun, kakakin hukumar yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya tabbatar.
Hakazalika, wani mutum dan shekara 60 a Ile-Ife, jihar Osun, Rafiu Irawo, ya kashe matarsa, Funke, kan zarginta da zina da wani mutumi sannan ya kashe kansa a ranar Juma'a, 20 ga watan Satumba, 2019. Gabanin haka, an tuhumci wata mata mai suna Akorede Balogun, da laifin kashe mijinta, Rasaki Balogun, a cikin gidansu dake No. 16, Taiwo Oke Street, Victory Estate, Ejigbo tare da wata karuwa, Muyibat Alabi, ranar 10 ga Yuli, 2019 a jihar Legas.
A jihar Ogun a Disamban, 2019, wani mutum mai suna Mutiu Sonola, ya shiga hannun hukumar yan sandan jihar kan laifin dukan matarsa, Zainab Shotayo, har lahira. Hakazalika ranar 27 ga Junairu 2020 misalin karfe 4 na Asuba, wata amarya ta burmawa mijin, Shamsuddeen Salisu, wuka har lahira a karamar hukumar Malumfashin jihar Katsina.
A karshe, binciken ya nuna cewa mata 36 sun rasa rayukansu ta hannun mazajensu yayinda maza 17 suka hallaka ta hannun iyalansu. Read more: https://hausa.legit.ng/1298289-maaurata-53-suka-kashe-kawunansu-tsakanin-nuwamban-2017-da-maryam-sanda-ta-kashe-mijinta-kawo-yanzu.html
DAGA ISYAKU.COM
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JC5tMMqXxKR6qWjM98ZwLA
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Twitter.com/isyakulabari