Ranar Laraba kotun koli za ta raba gardamar karshe tsakanin Buhari da Atiku

Legit Hausa
Labarin dake shigo mana da duminsa na nuna cewa kotun kolin Najeriya ta shirya tsaf domin yanke hukuncin karshe tsakanin zaben shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar All Progressives Congress APC da Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP.
Legit.ng Hausa ta samu labari daga bakin daya daga cikin lauyoyin jam'iyyar APC cewa kotun kolin za ta raba gardama tsakanin Buhari da Atiku ranar Laraba, 3o ga watan Oktoba, 2019.
A ranar 24 ga Satumba, 2019, Dan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, Atiku Abubakar, da jam'iyyarsa sun shigar da kara kotun kolin tarayya kan hukuncin da kotun zaben shugaban kasa ta yanke.
Lauyan PDP, Mike Ozekhome SAN, ne ya bayyana hakan.
A cewar Ozekhome, kotun zabe karkashin jagorancin Alkali Garba Mohammed, ta yi kuskure wajen tabbatar da nasarar shugaba Muhammadu Buhari.
Za ku tuna cewa a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, 2019 kotun zaben shugaban kasa na alkalai biyar sun yi ittifakin cewa karar da Alhaji Atiku Abubakar ya shigar babu kanshin gaskiya cikinta kuma sunyi watsi da ita.
Bayan kwashe akalla sa'o'i 8 a kotu, Alkali Garba Mohammed, ya tabbatar da shugaba Muhammadu Buhari matsayin zakaran zaben 23 ga Febrairu 2019.
DAGA ISYAKU.COM Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp https://chat.whatsapp.com/Hp4xUtixUxh5d76Kw2TGpp
Previous Post Next Post