Wata Kotun Majistare a birnin Illorin ranar Juma'a, ta tasa keyar wani dan acaba zuwa Kurkuku bisa zargin kashe wani kwastoma saboda N200 kudin haya.
Alkalin Kotun Mrs Jumoke Bello ta ki ta aminta da roko da wanda ake tuhuma ya yi, kuma ta tasa keyarsa zuwa Kurkukun Oke-kura da ke birnin Illorin kuma ta dage sauraron shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Aprilu.
Tun farko mai gabatar da kara na yansanda Sgt Kayode Roda ta ce ranar 23 ga watan Maris, wanda ake tuhuma ya dau fasanja daga Labe-Labe zuwa Fumuni amma sai fada ya kaure tsakaninsu saboda rashin daidaituwa game da kudin hayan acaba, sakamakon haka dan acaba ya zaro adda ya sare fasinja wanda ahakan haka ya yi sanadiyayar mutuwarsa.
DAGA ISYAKU.COM
Ku biyo mu a Facebook facebook.com/isyakunews
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/CM9VNSwQfZnIDKvffzvbiM
Domin GYARA wayarka ko FLASHING ka zo SENIORA TECH shago mai lamba 50 hawa na sama, TAUSHI PLAZA, Ahmadu Bello Way Birnin kebbi