Wa iyazu billahi, karanta abin da dan shekara 55 ya yi wa yarinya yar shekara 10

Wata babbar Kotun Majistire dake zamanta a babban birnin Minna na jihar Neja, ta bayar da umarnin garkame wani Dattijo a gidan kaso, Michael Itang mai shekaru 55 a duniya, bisa laifin yiwa wata yarinya 'yar shekara 10 fyade.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, ana zargin wannan Dattijo mai sana'ar Gadi da laifin keta haddi da kuma cin zarafin karamar yarinya. Jami'in dan sanda mai shigar da kara, ASP Daniel Ikwochie, ya shaidawa kotun cewa, a ranar Laraba 3 ga watan Oktoban da ya gabata, wata Mata Grace Tanko, wanda gidanta ke bayan babban Asibitin garin Suleja, tayi karar wannan Dattijo da ake zargi zuwa ga hukumar 'yan sanda.

Ikwochie tayi korafin cewa, Michael ya yaudari 'yar ta mai shekaru 10 kacal a duniya zuwa katarar dakinsa inda ya rinka murkushe ta tare da keta mata haddinta na 'ya mace. Rahotanni sun bayyana cewa, Dattijon ya rinka yaudarar wannan Yarinya da kudade tsakanin N20 zuwa N100 a duk lokacin da ya bukaci biyan bukatarsa ta kwazabar da namiji.

NAIJ.com ta fahimci cewa, laifin wannan Bawa mai muguwar zuciya ya sabawa sashe na 18 cikin dokokin kiyaye hakkin Yara na jihar Neja da aka kafa tun shekarar 2010. Yayin zartar da hukuncin sa Alkalin Kotun Nasiru Mu'azu, ya bayar da umarni ci gaba da garkame Itang a gidan Kaso tare da daga sauraron kararsa zuwa ranar 25 ga watan Oktoba kafin ta sake waiwayonsa.

Shafin mu na Facebook web.facebook.com/isyakuweb



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

KANA ZAUNE A BIRNIN KEBBI? WAYAR KA TA LALACE KO KANA BUKATAR FLASHING? 

Garzaya zuwa SENIORA TECH,shago mai lamba 50, hawa na sama gefen hagu,TAUSHI PLAZA , yamma daga gidan marigayi Waziri Umaru,kan Tiltin Ahmadu Bello, Nassarawa, Birnin kebbi. Barka da zuwa gidan sauki wajen gyaran wayar salula a garin Birnin kebbi.

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN