Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong ya sanya dokar ta
baci daga asuba zuwa faduwar rana a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta
Kudu biyo bayan rikicin da ya barke a kanan hukumomin da ya jawo mutuwar akalla
mutane 14 a safiyar Juma'a.
A cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mukaddashin
sakataren gwamnatin jihar, Sir. Richard Tokma ya bayyana cewa: "Biyo bayan
matsalar tsaro da aka samu a wasu sassa na karamar hukumar Jos ta Arewa, gwamna
Simon Bako Lalnog ya amince da sanya dokar ta baci daga karfe 6 na asuba zuwa 6
na yamma a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta kudu da ke jihar"
Sanarwar ta ce: "Yayin da gwamnati ke kokarin kare rayuka da dukiyoyin
jama'a, ana shawartar al'umma da su kwantar da hankulansu tare da bin dokar da
aka shimfida, da kuma bayar da rahoton duk wani motsi ko wani mutum da basu
yarda da shi ba ga hukumomin tsaro.
" Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa rikicin da ya
barke a wasu sassa na garin Jos a safiyar yau ya biyo bayan kashe wasu mutane 5
da kuma mata 8 a daren ranar Alhamis a sha-tale-talen Rukuba, kusa da Jos,
wanda wasu 'yan ta'adda suka yi.
Wannan kisan mutanen ya janyo hargitsi yayin da al'ummar da
abun ya shafa suka harzuka tare da toshe manyan hanyoyin da motoci ke wucewa
inda suke dirarwa fasinjojin da ke wucewa akan hanyoyin.
Jami'in hulda da
jama'a na rundunar yan sanda na jihar, DSP Tyopev Terna, a cikin wata sanarwa
ya bayyana ewa rundunar 'yan sanda sun samu kiran gaggawa don kai dauki a inda
lamarin ke faruwa inda ake harbe harbe a kan titin Rukuba kusa da Otel din Kowa
da ke Jos da misalin karfe 10:05 na daren Alhamis.
DSP Terna ya kara da cewa wadanda suka samu raunuka a harbe
harbe an garzaya da su asibitin koyarwa na jami'ar Bingham don basu kulawar
gaggawa, yayin da kuma rundunar tare da hadin guiwar sauran jami'an tsaro suka
samu nasarar fatattakar 'yan ta'addan.
Wakilinmu ya bayar da rahoton cewa zuwa yanzu an samar da
tsaro mai karfi a cikin garin na Jos, rikicin da ya sa aka tilasta iyaye zuwa
daukar yaransu daga makarantunsu. Kasuwanci da harkoki yau da kullum sun tsaya
tsak.
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Hausa.naija.ng
RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI