BOCA: Karanta abinda wata kungiya ta yi wajen tarbon Osinbajo a jihar Kebbi

Isyaku Garba | 8-9-2018 |

Kungiyar nan da ke karadin ganin shagaba Buhari da mataimakinsa Osinbajo sun sake cin zabe a 2019 reshen jihar Kebbi, Buhari Osinbajo Continuity Agenda, BOCA, ta shiga gangamin tarbon shugaba Buhari wanda maitaimakinsa Yemi Osinbajon ya wakilta a ziyararsa ta zuwa jihar Kebbi domin halartar addu'ar daurin auren Zakiya diyar Abubakar Chika Malami, Ministan shari'a kuma babban Atoni janar na Najeriya.

An daura auren da misalin karfe 2:43 na rana a babban Masallacin Sarkin Gwandu da ke kofar Fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu a garin Birnin kebbi.

Bayan gabatar da addu'a wanda Limamin Masallacin ya jagoranta a gaban Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, Mai Martaba Sarkin Gwandu da sauran manyan baki da suka hada da Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa'i, Gwamnan jihar Katsina Aminu Masari, tare da Gwamnan jihar Zamfara Abdul'azeez Yari. Hakazalika uban Amarya kuma Ministan shari'a Abubakar Chika Malami ya samu halartar taron addu'ar.

Saura sun hada da Ministan Ilimi, Ministan wasanni Solomon Dalong  da dai sauran manyan baki.

Tun farko dai,kungiyar BOCA reshen jihar Kebbi ta sami halartar tarbon Mataimakin shugaban kasa a babban filin saukar jirage na Sir Ahmadu Bello da ke Ambursa a jihar Kebbi. Shugaban kungiyar Alh. Mainassara Isyaka Katanga, Sakataren kungiyar Abu S. Aliyu, Darakta Socaila Media Abubakar Labaran Arab da Shugaban Mata na kungiyar Hauwa'u 'Yar Sarki tare da dimbin magoya bayan kungiyar duk sun halara a babban filin saukan jirage domin tarbon babban bako.

A zantawarsa da ISYAKU.COM Mahaifin Ango watau Alh. Aminu Maigishiri ya gode wa Allah da ya bayar da dama kuma wannan aure ya tabbata, ya kuma gode wa jama'a na gida da waje bisa wannan kyakkyawar halara tare da mutunci da suka nuna sakamakon zuwa wajen addu'ar daurin Auren.

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> whatsapp://chat?code=41x2TuRqdVQ9PrcrucqpTu Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN