An gano wata kabila a Najeriya da har yanzu ke sayar da ‘ya’ya mata


An samu wata kabila da ake kira “Becheve” a karamar hukumar Obanliku dake jihar Kuros Riba a kudancin Najeriya da har yanzu suke sayar da ‘ya’ya mata ko musayarsu domin biyan bashi.

Kabilar Becheve tayi suna a jihar Kuros Riba wajen yiwa ‘ya’ya mata dake da karancin shekaru auren dole. A wani faifan bidiyo da sashen yada labarai na BBC ya saki a shafinsa, wasu daga cikin irin wadanda suka tsinci kansu cikin irin wannan mawuyacin hali sun bayyana irin halin damuwa da bakincikin da suka shiga bayan sayar da su ko kuma yin kyauta ko biyan bashi da su.

Da take bayyana irin taskun da ta tsinci kanta, Dorothy, daya daga cikin irin yaran da suka tsinci rayuwar cikin wanna muguwar al’ada, ta bayyana said a jama’a suka taru don rike ta domin wanda aka bawa ita ya sadu da ita. Dorothy ta samu juna biyu kafin ta cika shekara 12 da haihuwa.

Kazalika wata yarinya, Happines, mai shekara 14 da wani tsoho mai jikoki ya say eta tare da mayar da ita matar sa duk da ba karancin shekarunta. Happiness ta bayyana yadda dattijon ke lakada mata duka tare da tuna mata cewar kudinsa ya saka ya sayo ta.

Wani malamin addinin Kirista, Fasto Akonam Richards, maza a kabilar ta Becheve na da ikon yin duk yadda suka so da yarinyar da suka saya ko aka basu a matsayin biyan. Sannan ya kara da cewar yanzu haka sun fara ceto wasu daga cikin irin wadannan yara tare da ganin sun kawo karshen wannan bakar al’ada da tuni duniya ta dade da dainawa.
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/AlFUDQouyehJRacXxBzbX0 Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira

Hausa.naija.ng

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN