• Labaran yau


  Karanta yadda wani fursuna ya tsere daga kurkuku da jirgi mai saukar angulu a Faransa

  Isyaku Garba | 2-7-2018 |

  Wani mutum da aka yanke wa hukuncin daurin shekara 25 a kurkuku, ya tsere daga gidan kurkukun Reau da ke kudancin birnin Paris, bayan wani jirgi mai saukar angulu ya dira a cikin harabar kurkukun dauke da wasu kwamandodi da ke dauke da mugan makamai suka dauke Redoine Faid's wanda ke zaune a dakin baki na gidan Kurkukun ranar Lahadi.

  Sanarwar haka ta fito daga ma'aikatan shari'a na kasar Faransa, haka zalika sanarwar ta ce babu wanda ya jikata kuma ba a yi garkuwa da kowa ba.

  Tuni dai 'yansandan Faransa suka kaddamar da gagarumin shirin neman Redoine wanda ke zaman Kurkuku bayan wata Kotu ta daure shi tsawon shekara 25 bayan ya kashe wata 'yarsanda a lokacin wani fashi da makami a 2010.

  Wannan ba shi ne karo na farko da Redoine ya tere daga Kurkuku ba, a shekara ta 2013 Redoine ya tsere daga wani Kurkuku bayan ya tarwatsa wani bangare na Kurkukun da nakiya da aka boye a wasu kwalayen tailet paper. Amma makonni shida kacal 'yansanda suka sake damke shi a cikin dakin wani Hotel.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Karanta yadda wani fursuna ya tsere daga kurkuku da jirgi mai saukar angulu a Faransa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama