• Labaran yau


  Gwamna Bagudu zai karrama sunayen 'yan jihar kebbi 2 da aka kashe a rikicin Jos

  Isyaku Garba | 3-7-2018 |

  Gwamnatin jihar Kebbi za ta karrama sunayen mutum biyu 'yan asalin jihar Kebbi, Zayyanu Gwandu da Zayyanu Shalla, wadanda aka kashe a rikicin Jos ranar 24 ga watan Yuni yayin da hanya ta biyo da su ta garin Jos daga Bauchi kan hanyarsu ta zuwa Abuja.

  Gawamna Atiku Bagudu ne ya shaida haka ranar Litinin, yayin da yake tarbon 'yan Majalisar zartarwa na jihar Kebbi da suka kai masa ziyarar taya shi murna bayan nassara da ya samu sakamakon hukuncin Kotu kan kalubalantar sakamakon zabe da aka yi masa.

  Bagudu ya kara da cewa gwamnatinsa zata kafa wata gidauniya ta zaman lafiya saboda a karrama sunayen wadannan 'yan asalin jihar Kebbi da aka kashe a kan lamari da basu ji kuma basu gani ba.

  Ya ce yin haka zai taimaka ya kara wayar da kan jama'a a kan illolin tashe-tashen hankali da rashin zama lafiya, kuma haka zai samar da dama domin kara fahimtar da jama'a a kan alhaerin zama lafiya a jihar Kebbi da kasa baki daya.

  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp >>> https://chat.whatsapp.com/Lq4Z5kPck53Le3ibU9RUnY
  Shiga cikakken shafin mu kai tsaye www.isyaku.com
  Tuntube mu ta SMS ko TEXT kawai zuwa 08087645001 ba mu amsa kira
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Gwamna Bagudu zai karrama sunayen 'yan jihar kebbi 2 da aka kashe a rikicin Jos Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama