• Labaran yau


  Babu karin albashi da tallafin man fetur a kasafin kudin 2018 - Danjuma Goje

  Shugaban kwamiti kasafin kudi a majalisar Dattawa Sanata Danjuma Goje ya ce babu tanadin karin albashin ma'aikata haka zalika babu tanadin rage kudin man fetur a kasafin kudi da Majalisar Dattawa ta aminta kuma aka gabatar wa shugaban kasa a kasafin kudi na 2018.

  Goje ya sanar da haka ne yayin da yake zantawa da 'yan jarida a Abuja ranar Laraba jim kadan bayan Majalisar ta aminta kuma ta rattaba wa kudurin hannu.

  Ya ce gazawar samun aiwatar da bukatun zai iya yuwuwa ne sakamakon rashin saka kudurin a cikin jerin bukatu a kasafin ababen da ake son a yi daga bangaren shugabanci.

  Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Babu karin albashi da tallafin man fetur a kasafin kudin 2018 - Danjuma Goje Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama