• Labaran yau


  Tallar dan siyasa a yanar gizo , ababen da ya kamata ka kula da su

  Kimiyyar zamani yana tafiya dadai da wayewar zamani haka zalika shafukan sada zumunta sun zama zaurukan isar da sako ko na addini, siyasa, kasuwanci ko ilimi da sauransu.

  Manyan kamfuna masu bayar da ayyuka ko gudanar da harkoki da ya jibanc mu'amala ta hanyar amfani da yanar gizo kamar Google,Yahoo suna bayar da bayanai ne ga jama'a yayin da Facebook,Whatsapp da sauransu ke sada mutane domin isar da sako bisa manufa.

  Amma a nan Najeriya, sau da yawa yan siyasa da yaran su ma'ana masu tallata su ga jama sai suka mayar da shafukan Facebook da Whatsapp wuraren kamfen marmakin sada zumunci ta hanyar bayar da bayanai na ilimi domin karuwa ko nishadi.

  MATAKIN FARKO, FUSKANTAR GASKIYA

  Yan siyasa na da kuduri da manufa wanda ya haifar da buri na ganin sun kai ga kujerar da suke so na ALFARMA kuma suna biyan masu tallata su a shafukan yanar gizo ta hanyar basu makudan kudade, saye masu motar shiga,kai su Makka ko a saya masu gida da dai sauran ababen kyautatawa.

  RASHIN GASKIYA DA TSARI

  Sakamakon haka sai wadannan yan tallan su fara sako hotuna da bayanan wadannan yan takaran a kowane zaure ko group da suka samu a yanar gizo musamman a whatsapp, ta hanyar cika zaurukan da hotuna tare da bayanan yan takaran wanda hakan ya saba wa ka'ida.

  ABIN DA ZA KA YI

  Idan kana da group a whatsapp kuma an dame ka da tallar yan siyasa, na farko dai sai ka bukaci a biyaka ihsani, na biyu idan an ki ko dai ka cire wanda ke turo maka wadannan hotuna da bayanai ko ka yi blocking na shi.

  KA TATTAUNA DA DAN SIYASAR

  Kana da dama da za ka iya tattaunawa da dan siyasa da yaronsa bisa tsari mai kyau. Ta haka za ka gayyaci duk yan group din ka idan kana a cikin garin da dan siyasar yake domin su ma a yi masu dan ihsani .Saboda suna amfani da kudinsu ne su sayi data amma sai yan siyasa su cika su da hotuna da bayanai wanda ke jawo assarar data.

  Daga Isyaku Garba

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Tallar dan siyasa a yanar gizo , ababen da ya kamata ka kula da su Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama