Jihar Kebbi: Kungiyar masu gyaran wayar salula zalla sun jaddada zamansu

Kungiyar masu gyaran wayar salula zalla na jihar Kebbi ta sake nanata zamanta tare da dogaro da kanta bisa turbar amana, mutunci, gaskiya da adalci tsakanin mambobin ta da al'ummar jihar Kebbi da Najeriya.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na jihar Kebbi Mal. Isyaku Garba wanda masani ne kan harkar ingizon wayar salula, masani kan harkar sadarwar tafi da gidanka na zamani , marubuci kuma dan jarida.

Mal. Isyaku ya bayyana wa yan jarida a sashen ofishin su na Correspndence chapel a unguwar GRA a garin Birnin kebbi cewa kanikawa masu gyaran waya ba masu sayar da waya bane, kuma aikwai banbanci tsakanin mai sayar da wayar salula da kuma mai gyaran wayar salula.Ya ce "Masu sayar da wayas salula 'yan kasuwa ne kuma lamuransu na kasuwanci ne amma masu gyaran waya injiniyoyi ne wadanda sukayi wa ilimi da'a aka koyar da su kafin su fara aiki a matsayin masu gyara".

Ya kuma bayar da misali cewa "akwai kungiyar masu sayar da motoci watau Vehicle Dealers Association na masu sayar da motoci kawai, akwai kuma kungiyar NURTW na masu jigilan fasinja a tashoshin mota sai kuma kungiyar kanikawan mota na Najeriya NATA kuma dukannin kungiyoyin nan suna magana ne a kan Mota, amma kowane bangare yana aikin sa bisa cancantar sa a bangaren da ya shafi rayuwarsa".

Mal Isyaku ya ce dokar Najeriya ta ba kowane dan Najeriya dama domin ya yi mu'amala da kowane kungiya da ya kwanta a ransa matukar kungiyar bata saba wa ka'idar Gwamnati ba. Sakamakon haka ya ce babu tilas akan cewa sai mutum ya shiga kungiyar, haka zalika ya shawarci duk wani mai gyaran wayar salula da bai yi rijista ba ya zo ya yi rijista da kungiyar domin samun albarkar kasancewa waje daya manufa daya wanda ta hakan ne kawai kanikawan wayar salula za su taimaki kansu harma su taimaka wa Gwamnatin jihar Kebbi ta hanyar baje basira da fasaha da Allah ya hore wa kanikawan wayar salula.

Daga karshe ya ce duk mai gyaran wayar salula da ke bukatar karin bayani zai iya tuntubar kungiyar a wannan lambar 08087645001.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN