• Labaran yau


  Mataimakin Gwamna Samaila Yombe wajen karrama wani jami'in dansanda

  Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Samaila Yombe Dabai ya halarci bikin karin girma da aka yi wa wani jami'in dansanda yau a hedikwatar yansanda da ke Gwadangaji a jihar Kebbi.Wanda aka yi wa karin girma Umar Musa ya sami karramawa daga kwamishinan yansanda na jihar Kebbi CP. Ibrahim Kabir.

  Yombe ya shawarci hafsan da aka yi wa karin girma ya ci gaba da kasancewa mai da'a da aiki tukuru domin ci gaba.Kwamishi Ibrahim Kabir ya gode wa Mataimakin Gwamna akan karramawa da ya yi na halartar wannan lamarin na karin girma.


  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mataimakin Gwamna Samaila Yombe wajen karrama wani jami'in dansanda Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama