• Labaran yau


  Kalli yadda miji ya daddatsa matarshi da adda kuma ya kashe kanshi

  Wani mutum ya kashe kanshi bayan ya sassare matarshi da adda a jihar Delta. Matar mai suna Mr.Promise tana kwance a cibiyar kula da marasa lafiya na tarayya da ke Asaba inda take jinyar sara da mijinta ya yi mata da adda da yammacin ranar Litinin.

  Wata majiya ta labarta cewa matar ta dawo daga tafiya ne da yammacin ranar, ba tare da sanin manufar mijinta ba daga shigar ta gida sai mijin ya fara saran ta da adda .

  Ganin haka ya sa dansa ya yi kururuwa da ya sa makwabta suka kawo taimako kuma aka kira yansanda. Isar yansanda ke da wuya sai suka gan mutumin kwance a kasa babu rai.

  Tuni dai aka kai gawarsa dakin ajiye gawa a wani Asibiti da ba'a fadi sunan sa ba.

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kalli yadda miji ya daddatsa matarshi da adda kuma ya kashe kanshi Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama