Kalli wani barawon babur da aka kama bayan ya saci babur a Asibiti

Hausawa sun ce dare dubu na barawo dare daya na mai kaya, haka yake domin dai Allah ya tona asirin wani bawansa da ya saci wani babur kirar roba-roba a Asibitin jihar Gombe jiya.

Nan take jami'an tsaro na Asibitin suka damke shi bayan sun yi masa tambayoyi sai kuma suka mika shi ga jami'an 'yansanda.

Satan babur dai ya zama ruwan dare musamman a yankin Arewacin Najeriya kuma wani lokaci su barayin baburan ne ke kashe masu acaba musamman kamar yadda aka sami labarin wasu 'yan acaba da aka kashe a jihar Kebbi a lokuta daban-daban a 2017.

Haka zalika jama'a kan mayar da martani ta hanyar kashe wadanda ake zargi da satan babur kamar yadda aka kashe wanda ya saci babur a wani Banki a garin Birnin kebbi, da wanda ake zargin ya saci babur a Danko-Wasagu da kuma wanda ya saci babur a Masallacin Juma'a yayin da ake Sallan Juma'a a Masallacin Sarkin Yauri wanda dukkansu tare dawasu barayin baburan aka kashe su mutus wani ma har kone shi aka yi.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN