Labaran Duniya Laraba 13/12/2017 (Yamma)

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya roki wadanda su ka bar jam’iyyar PDP zuwa APC da su ka hada da Rabi’u Musa Kwankwaso, da Bukola Saraki, da Aminu Waziri Tambuwal su dawo jam’iyyar su ta asali.

Atiku Abubakar, ya ce babu sauran wata jam’iyyar siyasa a Nijeriya in ba jam’iyyar PDP ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa ya bayyana haka ne a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Abuja.

Idan dai za a iya tunawa, a watan da ya gabata ne Atiku Abubakar ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP.

Kungiyar Dattawan Arewa ta musanta rahotannin da kafofin yada labarai su ka yada cewa sun bada shawarar sake tsayar da shugaba Buhari a matsayin dan takara karo na biyu.

A wata hira da ya yi da manema labarai, an ambato shugaban kungiyar Paul Unongo ya na cewa, yankin Arewa ya tsayar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takara a zaben shekara ta 2019.

Sai dai daya daga cikin jiga-jigan kungiyar Captain Bashir Sodangi, ya ce duk abin da Unongo ya fada ra’ayin kan shi ne ban a kungiya ba.

 Ya ce kungiyar ba ta taba tattaunawa game da siyasar shekara ta 2019 ba balle ta tsayar da dan takara.

Wasu 'yan bindiga sun kai hari gidan gonar shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati.

Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne ranar Talata da misalin karfe goma na dare.


Gidan gonar yana yankin karamar hukumar Karshi ne da ke wajen babban birnin tarayya.
Kakikin hukumar EFCC, Wilson Uwajuren da takwaransa na rundunar 'yan sandan Abuja, Anjuguri Jesse Manza sun ki tabbatar ko musanta aukuwar lamarin, a lokacin da BBC ta tuntube su.


Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewacin Najeriya, Abdullahi Adamu ya ce, rashin adalci ne a yi dakon shugaban kasar Muhammadu Buhari wajen aiwatar da shawarwarin da aka tattara a rahoton taron hadin-kan-ƙasa da aka gudanar lokacin mulkin Goodluck Jonathan a shekarar 2014.

Adamu ya bayyana haka ne gabanin bude taron Ƙungiyar Sanatocin da yanzu haka ke gudana a jihar Katina da ke arewacin kasar don tattaunawa kan matsalolin da suka hada addabi arewa da kasar baki daya.


A cewar Adamu, babu yadda za a tilasta wa Buhari aiwatar da rahoton da aka fitar bayan taron hadin-kan-Æ™asar, musamman ma idan aka yi la’akari cewa, shugaban ba shi da hannu a rahoton.


Taron na yau wanda ya samu halartar Sarakunan gargajiya, zai kuma tattauna kan fafutukar sake fasalta Najeriya da kuma batun kasafin kudi baya ga matsalar tsaro a wani sashi na arewacin kasar.


Sanatoci 58 ne daga shiyoyin arewa uku ke halartar taron na yau.


Kazalika gwamnonin jihohin Kebbi da Zamfara da Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar da wasu daga cikin manyan mutane sun halarci taron.

Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com *** GURBIN TALLA *** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN