• Labaran yau

  Mu dinga yi wa juna fatan alhairi,buri na shine in yi aure - Jamila ruwa baba

  Hajiya Jamila Ruwa Baba Fitacciyar Mawakiya ce da ke zaune a garin Birnin Kebbi, 'yar asalin karamar hukumar mulki ta Zuru wacce ta yi suna sakamakon wakar siyasa ta "Ruwa Baba" a zamanin mulkin Sa'idu ta bayyana mana yadda take ganin rayuwa.

  Jamila da ta fara sana'ar waka kimanin shekara goma da suka gabata bata da Aure amma ta nuna sha'awar yin Aure idan Allah ya kaddara ta sami Miji

  "Wakar Ruwa ruwa baba ita ce waka da ta zama mini bakandamiya domin ita ta jawo mini daukaka"

  Duk da yake Jamila bata da Studio na tsara wakoki nata na kanta , ta tabbatar mana cewa wannan baya a kan ta yanzu haka.

  "Wasu wakoki a da ni ke rubuta su da kaina ,amma yanzu na raggonta akan haka , nikan sa ne a rubuta mini ,amma rerawa, da kirkiro sauti ni ke yi da kaina, kuma babban buri na a rayuwa a yanzu haka shine in ga kaina a gidan Miji na.Da yake na fara gina ina rokon Allah ya bani iko in ga na gama gini na kuma in yi Aure su ne babban buri na guda biyu a yazu".

  Mawakiya Jamila ta ce ba gaskiya bane cewa Mawaka na jihar Kebbi basu da hadin kai, ta kara da cewa Mawaka suna da kungiyarsu ta Mawaka wacce ke gudanar da lamurran ta cikin zumunci.Ta kuma kara da cewa ai idan akwai wani biki ko na Gwamnati ko ba na Gwamnati ba sukan je gaba dayan su su Mawaka "Ka ga idan babu hadin kai tsakanin Mawaka ba za ka gan mu ba gaba dayan mu a wajen bukukuwa, gaba dayan mu zaka gan mu a wajen biki idan an gayyace mu".

  "Ina rokon jama'a cewa yadda kake son kanka ka so 'danuwan ka, domin shi sana'a duk inda Allah ya aje ka babu yadda za ka yi da shi, idan Allah ya ce kashi zaka dinga kwasa ka ci abinci da shi haka zai kasance.Sa'annan sana'ar waka idan ka duba da kyau mara ilimi baya yin sa.Saboda haka ina rokon mutanen mu su yi hakuri mu dinga kallon juna iri daya , mu so junan mu kuma mu daina yi ma junan mu mugun kallo.Gaskiya sana'ar da muke yi ba mugun sana'a bane sana'a ne na wahala idan mutum ya duba gaskiya.Sakamakon haka ina neman alfarman mutane a daina yi mana kallo na daban ko ana yi mana zargi da ba haka bane".

  Jamila ta roki jama'a cewa "Mu so junan su kuma mu dinga yi ma junan mu fata na gari shawara ta kenan daga karshe".

  Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mu dinga yi wa juna fatan alhairi,buri na shine in yi aure - Jamila ruwa baba Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama
  .disablecopypaste { -webkit-user-select: none; Chrome/Safari/Opera/Opera mini -moz-user-select: none; Firefox -ms-user-select: none; Internet Explorer/Edge -webkit-touch-callout: none; iOS Safari} And in your html:

  This text can’t be copied (cannot be selected).

  // Deactivating distracting Text Selection: // from: http://stackoverflow.com/questions/1794220/how-to-disable-mobilesafari-auto-selection $.fn.extend({ disableSelection : function() { this.each(function() { this.onselectstart = function() { return false; }; this.unselectable = "on"; $(this).css('-moz-user-select', 'none'); $(this).css('-webkit-user-select', 'none'); }); } }); $(function() { $(this).disableSelection(); });