Header Ads

Maza sun shiga tsoro kilan matan su za su kashe su - Bincike

Sakamakon wani bincike da aka gudanar a jihar Lagos ya nuna cewa yanzu haka da yawa daga cikin Maza suna tsoron cewa Matan su za su iya kashesu.Wannan sakamakon ya fito ne bayan matsalar da aka samu tsakanin marigayi Bilyamin da matarsa Maryan lamari da ya zama babban labari a kafofin watsa labarai a Najeriya.

Wani kididdiga da Gwamnatin jihar Lagos ta fitar dangane da adadin yawan koke da ake samu sakamakon tashin hankali tsakanin Ma'aurata a jihar ya nuna cewa Mata ne suka fi shan wuya a wannan lamari domin a cikin koke 852 da aka gabatar a tsakanin watanni tara da suka gabata 55 ne kawai Maza suka shigar yayin da sauran Mata ne suka koka.

Wata ma'aikaciyar Asibiti a garin Birnin Kebbi da bata son a ambaceta ta shaida wa ISYAKU.COM cewa "Ni a nawa fahimta ,Mata ne ke jawo lamarin da ke kaiwa ga tashin hankali ko fitina a cikin gida,domin idan har kina bin Maigidan ki sau da kafa, babu yadda za'ayi har ace yau lamari ya kazamce har ya kai ga tashin hankali".

"Da farko dai Mace bata da hurumin binciken wayar Mijinta idan har Matar gaskiya ce mai son zaman lafiya, na biyu raini da neman ganin laifin Miji, sai wulakanta miji ta hanyar cin mutunci ko rashin ragowa wajen furta kalamai.Sakamakon haka Miji zai iya tunzurewa musamman ga Mata wadanda ke kaiwa ga cukume rigar Maigida, ka ga daga nan raini ya shiga shi kuma Maigida dole ne ya kubuta sakamakon haka sai dambe da tashin hankali ya kaure" .

Duk da yake wannan lamari ya zama ruwan dare a ko'ina cikin fadin Najeriya, amma kasancewar irin wannan lamarin ya fi yawa a Arewacin Najeriya, idan baku manta ba,mun kawo maku labarin wata mata da ta tafasa ruwan zafi ta zuba wa Mijinta da Amaryarsa a jihar Kaduna yayin da suke barci wai domin ya yi mata kishiya lamari da ya sa Mijin ya rasa ransa kwanaki kadan bayan jinya.

Haka zalika mun kawo maku labarin Matar da ta caka wa Mijin ta wuka sakamakon yunkuri da ya yi na kara aure wanda hakan ya zama ajalinsa a jihar Niger.

A jihar Kano kuwa mun kawo maku labarin wacce ta kashe maigidanta bayan ta saka masa abincin bera a cikin nashi abinci sakamakon haka ya mutu.

Haka zalika ga labarin Bilyamin da Maryam da ta kashe Bilyamin a gidansu da ke Wuse a Abuja da kuma labarin wadda ta kwada wa mijinta kwalba a kai sannan ta yi amfani da tsinin kwalbar ta caka masa a kirji a jihar Zamfara.

Ina mafita ne akan wannan lamari ? rashin aiwatar da hukunci ne ko kuwa son ra'ayi ne ke samar da tunani balle dama da ke sa mutum ko mace ta yi tunanin cewa za ta iya kashe maigidanta kuma babu abun da zai faru ?.

**************************************** Tuntube mu ko aiko Labari zuwa isyakulabari@gmail.com Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com **************************************** Kana son ka yi flashing ko ka cire makulli watau security na wayar ka? ka zo SENIORA TECH a OLUMBO PLAZA yamma da Gidan Wazirin Gwandu kan titin Ahmadu Bello a garin Birnin Kebbi. Shago Lamba 51 hawa na sama.
Powered by Blogger.