• Labaran yau

  Jandarman Cameroon sun yi sanadin mutuwar 'yan Najeriya 2 sakamakon rikicin fili

  Gwamnan jihar Cross River Ben Ayade ya kafa wata tawaga mai karfi domin ta sasanta tare da shawo kan wani rikici da ya bullu a yankin Danare 2 a karamar hukumar Nokia tsakanin mazauna yankin da mazauna wasu kauyuka makwabta daga bangaren kasar Cameroon.

  Bayanai sun nuna cewa wasu Jandarma daga bangaren kasar Cameroon sun ketaro zuwa yankin Najeriyata ta garin Danare suka tayar da hankalin mazauna yankin sakamakon rikicin fili a rikicin da ya kai ga halaka mutun biyu tare da jikata wasu mutum shida.

  Tawagar ta hada da mai ba Gwamna shawara kan harkar tsaro Mr.Jude Ngaji,Kwamishinan 'yansanda Mr.Hafiz Inuwa da shugabannin Matasan yankin yayin da aka jibge jami'an 'yansanda domin tabbatar da tsaro.

  Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Jandarman Cameroon sun yi sanadin mutuwar 'yan Najeriya 2 sakamakon rikicin fili Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama