B-kebbi: Kurame sun bukaci gwamnatin jihar Kebbi ta dinga damawa da su (Hotuna)

A yau kungiyar kurame na jihar kebbi karkashin jagorancin Mal.Umar Mai nama Sarkin kuramen Gwandu sun gudanar da wani takaitaccen tattaki rike da kwalaye da ke dauke da rubutun bukace bukacensu ga gwamnatin jihar Kebbi.

Kuramen sun ja burki a kofar gidan gwamnatin jihar Kebbi inda suka koka akan abinda suka kira rashin cika alkawari da gwamnati tayi masu tare da bukatar a duba lamarinsu da idon basira daga bisani sun bayar da takarda zuwa ga Gwamnan jihar Kebbi Alh.Atiku Bagudu.

Kuramen sun rubuta cewa lalurar kurumta abu ne daga Allah kuma bai kamata a dinga tsangwama ko nuna masu wariya ba.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN