An kama soji 3 bisa zargin satar na'urar sarrafa hasken rana na N100m

Wasu soji uku da korarren sojin sama tare da wani 'dalibi sun fada hannun jami'an 'yansanda bisa zargin satar na'urorin sadarwa da tasar sarrafa hasken rana wanda aka kiyasta kudinsu akan Naira Miliyan dari N100m.

An kama mutanen ne a unguwar Epe a garin Lagos yayin da aka mika sojin guda uku ga rundunar soji ta 9 domin ci gaba da bincike.Shi kuma korarren sojin sama Odafuye cewa yayi an kore shi daga soja ne bayan matsala da ya samu a Maiduguri inda ya ke fada da boko haram.

Wadanda aka kama sun hada da Samuel Ani (30), Michael Omoregbe (30), Efosa Philip (27),korarren sojan sama Ifedayo Odufoye (35), Chibize Nnamani (34), Festus Maduka (26), John Nwokeoma (31), Michael Chukwudike da Chibuzor Chukwu (23).


Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN