An ceto mataimakin kwamishinan 'yansanda da aka sace

Tawagar fitaccen 'dan sandan nan masani kan aikata manyan laifuka ACP Abba Kyari yayi nassarar kubutar da mataimakin kwamishinan 'yansanda da 'yan bindiga suka sace shi kuma suka yi garkuwa da shi ranar 27 ga watan Satumba akan hanyar Dandume/Birnin Gwari  (Katsina/Kaduna).

Emmanuel Adeniyi shi ne mataimakin kwamishinan 'yansanda mai kula da sashen bincike CIID a jihar Zamfara kuma an kama shi ne tare da iyalinsa mutum uku yayin da suke a cikin wata mota kirar Hilux.

An ceto ACP Adeniyi ranar Asabar 30 ga watan Satumba bayan Kyari da tawagarsa ta musamman sun tsunduma wajen neman wadanda suka sace babban jami'in 'dansandan.

Bayanai sun nuna cewa 'yan bindigan sun nemi fansar Naira Miliyan 50 da farko,amma ba'a bayar da ladar ko kwabo ba kafin a ceto ACP Adeniyi.

Ga masu shawara,aiko labari ko korafi ku rubuto zuwa isyakulabari@gmail.com Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN