Shugaba Buhari, ka duba bukatun Arewa kafin lokaci ya kure (1) - Isyaku Garba

Najeriya kasa ce da ta kunshi kabilu da addinai kala-kala da miliyoyin mutane masu hali daban-daban wadda tasirin halayen diyanta suka janyo mata suna kala biyu a idon Duniya.

Na farko dai shine an shaida dan Najeriya da kwazo a duk inda ya sami kansa,a daya bangaren kuma shine dan Najeriya ya sami kyakkyawar shaidar kasancewa mazambaci,ga taurin kai da kin son gaskiya ga damfara da cin amana kamar yadda mujallar TheWatch ta wallafa.

A cikin irin wannan daula mai jama'a fiye da miliyan 180 aka sami shugaba wadda ya taba dandana mulkin Najeriya sa'ilin da yake da damarar kakin Soja amma bai yi karko ba sakamakon cin amana daga 'yan uwanshi Sojoji a waccan lokacin.

Yau wannan bawan Allah ya kasance shugaban kasa ta hanyar zabe na Dimokaradiyya,wannan talikin shine Janar Muhammadu Buhari (mai murabus) Lokacinda Buhari ya tsaya takara na zabe shi akan cewa Musulmi ne,Bafillace dan Arewa domin a waccan lokacin na kula da irin barna da ke da asali da kabilanci da aka dasa a Gwamnati da Buhari zai kara da ita a wajen zabe na 2015.

A kwana a tashi Buhari ya zama shugaban kasa,amma har yanzu da sauran rina a kaba domin abin yana bani mamaki ganin cewa har yanzu shekara biyu da yan kai ba'a fara maganar daidaita barnar da Gwamnatoci da suka shude suka yi wa Arewa ba,ina zance ne akan yadda aka sallami dubu dubatan 'yan asalin Arewa daga aikin tsaro ta bangaren Sojan sama,na kasa,na ruwa da 'yansanda.

A bangaren hukumomin ayyukan asiri da harkokin leken asiri na kasa kuwa,lamarin ya fi muni saboda sai da aka zabi kwararru da shahararru yan asalin kasar Arewa kafin aka sallame su  daga aiki wadda hakan yayi wa kasar Arewa mumunar illa ta bangaren tsaro sakamakon abinda kowane dan Najeriya ya sani ne game da yankin Borno,Yobeda Adamawa.

Yanzu ne lokacin Arewa domin sanin gobe sai Allah,a bisa wannan daliline nike rokon shugaba Muhammadu Buhari ya bude bincike akan yadda aka sallame jami'an leken asiri na NIA da DSS tun daga 1999 zuwa 2015 na yi imanin sakamakon binciken zai bayar da mamaki.

Na kuma yi roko akan cewa ayi kididdiga yawan ma'aikata da ke NIA da DSS kuma a fayyace mutum nawane kowace jiha take da su nawa ne 'yan Arewa kuma nawa ne 'yan kudu,nawa ne Musulmi nawa ne Kirista.Gaskiya zaku sha mamaki sakamakon da zai biyo baya.

Yayin da akwai manya manyan kura kurai da ya kamata a gyara kafin 2019,an shafe fiye da shekara biyu ana bincike,tabbas bincike ya haifar da da mai ido domin ga Kotu ta yanke hukunci a kwace wasu kudade da kadarori daga wasu azzalumai da suka damfari Najeriya.Amma ina son in tuna wa shugaba Buhari wasu kalamai  da tsohon shugan kasa Olusegun Obasanjo yayi inda yace "Allah kadai ne zai iya gyara halin dan Najeriya ".

Saboda haka a yanzu shugaba Buhari kaine gatan Arewa,yayin da ka dukufa wajen yaki da barayin dukiyar talakka,yana da kyau ka duba bukatun Arewa kafin lokaci ya kure kamar yadda ya faru 1983 da shugaba Shehu Shagari da ya dukufa wajen raya kasar kudu a zagayen shugabancinsa na farko da niyyar ya gyara Arewa a karon mulkinsa na biyu dama da bai samu ba kenanba har akayi juyin mulki Arewa tayi asara.

Don Allah shugaba Buhari ka sake duba wadannan bukatu na Arewa:

1  Aikin jawo ruwan teku daga kudu zuwa Arewa har zuwa kasar Lokoja kamar yadda marigayi shugaba Yar Adua ya bukaci yayi a zamaninsa.

2  Ka daidaita yawan jami'an tsaro da aka rage wa Arewa

3  A hanzarta kammala manyan hanyoyin mota da na jirgin kasa a nan Arewa

4  A sake farfado da aikin neman man fetur a yankin Arewa bayan wadda aka  samu a yankin Borno da yankin tafkin Tchadi

5  A maido da kayan yakin Sojojin Najeriya da Gwamnatin Obasanjo da na Jonathan suka dauke daga Arewa zuwa kudu a maido su inda suke a da watau Kaduna.

6  Idan har Gwamnati za ta adana El-zakzaky da Sambo Dasuki  bisa dalilai na tsaro lallai Gwamnati tayi maganin Nnamdi Kanu bisa barazanar da yake yi wa Arewa da Najeriya

Isyaku Garba ,Edita ISYAKU.COM


Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN