Mata ku rika tausaya wa mazajen aurenku!

Wani mutum ne da matarshi da ya'yanshi suke zaune cikin jin dadi da walwala....yanada kudi da yake ba mai kankamo bane yana sakar musu sosai..basu nema sun rasa ba.

Hakanan kawai duniya tai masa juyin waina,abinda ma zasuci ya zama da kyar ake samu.Wataran suka tashi basu da abinda zasuci sai suka fita nema shi da matarsa, yana tsaye yana tunanin inda zashi, kwatsam sai ga masu neman tsofaffin kayan karfe ya taho, maigida ya tuno da tsofaffin gwangwanayensu na madara da na Milo danasu bournvita, da murnarshi ya tsayar da mutumin ya shiga gida ya debo masa ya siya ya bashi yan kudadensa.

Da murnarsa ya siyowa ya'yansa gari suka jika suna sha...suna tsakar shan gari  sai matarsa ta dawo, ta
zauna tana tambayarsa ina suka samu garin da suke sha?da fara'arsa ya mika mata nata yana bata labarin gwangwanayen da ya siyar kawai sai matar ta zabura ta mike tana zunduma ihu tana fadin ta shiga uku...maigidan ya rude yana tambayarta abinda ya faru da kyar ta iya fadin a cikin gwangwanin akwai kudinta dubu dari biyu da hamsin....!!!

Mai za'a kira wannan matar dashi ?

Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN