Jihar Kebbi ta mayar da shirin tsabtace gari na karshen kowane wata

Bayan bullar cutar amai da gudawa  da yayi sanadin rayukan mutum 20 a jihar Kebbi,Gwamnatin jihar Kebbi ta farfado da aikin tsabtace gari na wata wata wadda za a fara gudanarwa a ranakun Asabar na farko ko karshen kowane wata.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Kebbi Alh.Musa Kalgo ya shaida haka yayinda yake zantawa da manema labarai ranar Alhamis a Birnin kebbi ya kuma kara da cewa za'a dinga gudanar da shara a ranakun Asabar na karshe ko na farko a kowane wata daga karfe 8:00 am zuwa 10:00 am na safe.

Kalgo ya bukaci jama'a su bayar da goyon baya ga tsarin Gwamnatin jiha domin tabbatar da samun nassara wajen tafiyar da shirin.

Kwamishinan ya kara da cewa "An lura jama'a na ko in kula da yanayin tsabtar muhallinsu da kewaye lamarin da kan haifar da barazana ga lafiyar al'umma"

Kaunace mu a Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a SMS zuwa 08087645001. Shiga cikakken shafinmu. www.isyaku.com

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN