Yadda wani makahon karya ke samun N8000 a kullum

Abdullahi Abbas wani makahon karya ne da ya dade yana kwaikwayon cewa shi makaho ne kuma a bisa hakan ne yasa wani yaro dan shekara 12 ke janshi da sanda domin ya bi da shi hanya.

Abdullahi dai dan shekara 37 wadda ke gudanar da harkarsa ta bara a unguwar First Gate da Odogunyan a yankin Ikorodu da ke birnin Lagos.

Bayanai sun nuna cewa takaddamar da ta taso tsakanin wata mace Adeoye Baliks da shi Abdullahi ya kaiga bankado cewa ashe Abdullahi ba makahon gaske bane.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Abdullahi dan asalin jihar Oyo ne kuma ya shaida wa yansanda cewa yakan sami N5,000 zuwa N8,000 a kullum daga aikin bara da yake yi.

Yan banga sun kamashi kuma suka mika shi ga hukumar yansanda.


Shafin mu na Facebook
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN