Dododo ya alakanta wannan matsalar akan lalacewar wani bangare na na'urar transfoma 7.5kva dake unguwar byepass a garin Birnin kebbi.
Ana kyautata zaton cewa injiniyoyi masana daga Kaduna zasu zo domin su duba matsalar da Dododo yace Gwamnatin jihar Kebbi zata taimaka da abinda ya wadata domin a shawo kan matsalar.
Ya kuma bukaci jama'a su kai rahotu matukar sun lura da wata matsala da ta shafi wuntar lantarki ga jami'an Kamfanin Kaduna Electric a ofishinsu.
Shafin mu na Facebook https://www.facebook.com/isyakuweb Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120. Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.