Jawabin shugaba Buhari - "zan yaki mugaye da 'yan ta'adda "

Ya ku 'yan uwana 'yan Najeriya.

Ina mai matukar godiya ga Allah da kuma daukacin 'yan Najeriya saboda addu'o'in da suka yi mini. Ina farin cikin dawowa gida cikin 'yan uwana maza da mata.

Yayin da nake jinya a kasar Birtaniya, ina samun labaran abubuwan da ke faruwa a gida.
'Yan Najeriya suna tattauna al'amuran da suke faruwa, amma na fahimci cewa wasu daga cikin kalaman da ake yi musamman a kafofin sada zumunta sun ketara iyakar dokokin kasar nan inda suke sanya alamar tambaya game da ci gaba da kasancewarmu a matsayin kasa guda. Wannan wani abu ne na wuce gona da iri.

A shekarar 2003 bayan da na shiga siyasa, marigayi Cif Emeka Ojukwu ya taba ziyarta ta kuma ya zauna wurina a Daura. 

Mun kwashe fiye da kwana biyu muna tattauna matsalolin Najeriya, a wasu lokutan mukan shafe dare muna magana. A karshe mun cimma matsayar cewa wajibi ne Najeriya ta ci gaba da kasancewa kasa daya kuma dunkulalliyya.

Hadin kan 'yan Najeriya wani abu ne da aka cimma matsaya a kai. Kuma ba ya bukatar a sake waiwayarsa.

Ba za mu bari wasu marasa dattako su fara tada fitina kuma idan abubuwa suka lalace su gudu su bar wasu da aikin dawo da doka da oda, wata kila ma hakan ba zai yiwu ba sai an zub da jini.
Kowane dan Najeriya yana da 'yancin rayuwa da kuma gudanar da harkokinsa a ko ina a Najeriya ba tare da an yi masa wani shamaki ba.

Na yi amannar cewa dimbin 'yan Najeriya suna da irin wannan tunani.
Sai dai wannan ba yana nufin cewa babu kwararan batutuwan da suke damunmu.
Kowane bangare yana da korafinsa. Amma dadin tsarin da ake tafiyar da kasar a kai yanzu shi ne, yadda ya tanadin hanyoyin da duk wadanda suke ganin an yi musu ba daidai ba, za su iya gabatar da korafinsu da kuma yadda za a ci gaba da tafiya tare.

Majalisar dokoki ta kasa da kuma majalisar koli ta kasa su ne wuraren da doka ta yarda a tattauna manyan batutuwan da suka shafi Najeriya.

Baki ya zo daya a kasa baki daya cewa ya fi kamata a ci gaba da zama tare maimakon a raba kasar.
Bugu da kari, ina kira da rundunonin tsaro da kada nasarar da aka samun a watanni 18 da suka gabata ta sa su, su rage kaimi.

Wajibi ne mu yaki 'yan ta'adda da miyagu kuma mu ga bayansu saboda mu ci gaba da rayuwa cikin zaman lafiya da tsaro.

Wannan ya sa za mu kara kaimi ba kawai a yaki da 'yan Boko Haram ba wadanda suka fito da sabbin hanyoyin kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba hari. 

Hakazalika za mu sa kaimi a yaki da masu satar mutane don neman kudin fansa da rikicin Fulani makiyaya da manoma da rikicin kabilanci wanda wasu 'yan siyasa masu munanan manufa suke rura wutarsa. Za mu magance su duka.

A karshe 'yan uwana 'yan Najeriya abin da ya dace yanzu shi ne mu manta da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu fuskanci wadannan kalubalen da suka shafe mu duka; wato gyara tattalin arziki da bunkasar siyasa da hadin kan kasa, har ila yau, da samar wa 'yan Najeriya dawwamanman zaman lafiya.

A shirye nake don ganin mun cimma wannan burin da kuma ganin dorewarsu. Ina farin cikin dawowa gida.

Na gode kuma Allah Ya albarkaci kasarmu.


Shafin mu na Facebook
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu.
Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN