Birnin kebbi - Me ya sa marasa gaskiya ke tsoron Kotun Alkali Mu'awiyya ?

Rashin aiwatar da hukunci  ga mai laifi wani abu ne da masu kula da yadda lamurra ke tafiya kallon dama da kan sa mai aikata laifi ya sake aikata laifin ko kuma ya mayar da aikata laifin tamkar wata dama da yake da ita na yin yadda yake so kuma babu yadda za'ayi da shi.

A wani bincike da ISYAKU.COM ya gudanar a cikin garin Birnin kebbi a Kotuna da ake gabatar da masu laifi,sakamakon binciken mu ya nuna cewa babu wata Kotu a cikin garin Birnin kebbi da marasa gaskiya ke tsoron zuwa kamar Kotu ta 1 da Mai shari'a Alkali Mu'awiyya ke Alkalanci.

Sakamakon binciken namu har ila yau ya nuna cewa a laifuka kamar sata,luwadi,fyade da sauran laifuka da suka jibanci ajin laifuka da muka ambata ,Alkalin yakan garzaya da mai laifin ne zuwa gidan Yari matukar masu gabatar da kara sun tabbatar ta hanyar gabatarwa a gaban Kotu laifi,kamar ga barawo ga abinda ya sata ga wanda aka yi wa satar ga shaidu amma kuma wanda ake zargi ya musanta a bisa hurumin doka Mu'awiyya yakan adana mai laifin akalla koda mako  daya ne a gidan kurkuku.

Wannan matakin yayi tasiri ba kadan ba akan wasu marasa gaskiya a cikin al'umma.

Hakazalika marasa gaskiya su kan  yi iya abinda zasu yi domin su kauce wa zuwa kotun Alkali Mu'awiyya saboda a kowane lokaci aka sami matsala da wanda ya saba aikata laifi binciken mu ya gano cewa mai laifin da 'yan uwansa sukan yi iya kokarinsu domin neman sasantawa ko tabbatar da cewa ba a kai su gaban Kotun Alkali Mu'awiyya ba saidai a kai su wata Kotun daban.

Me yasa hakan ya kasance ne tsakanin wasu masu laifi da Kotu ta 1 a garin Birnin kebbi? ....lokaci ne kadai zai iya tabbatar da wannan amsa.


Daga Isyaku Garba- Birnin kebbiKu biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120. Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN