Wani shugaba a jam'iyar APC ya sha dukan tsiya a jihar Delta

Yayin da fagen siyasar Najeriya ke ci gaba da kasancewa fagen dambaruwar ababen kunya da rashin ragowa ga su  kansu 'yan siyasa,wani shugaban jam'iyar APC a karamar hukumar Uvwie a jihar Delta ya sha dukan tsiya a hannun 'yan bangan siyasa wanda bayan sun likida masa duka suka kuma tube shi zindir.

Mr Eddy James Onajite shine shugaban jam'iyar APC a ward na 8 a karamar hukumar.

Bayanai sun nuna cewa 'yan bangan siyasa da suka tare tawagar Sanata Ovie Omo-Agege kuma suka ci zarafinsa ranar Asabar da ya gabata sune kuma suka aikata wannan danyen aikin wa shugaban na APC a karamar hukumar Uvwie.

Haka zalika a garin Birnin kebbi,a 'yan makonnin da suka gabata wani matashi mai suna Muhammed Bello ya sha duka a hannun wani dan bangan siyasa da ke tare da wani dan siyasa sakamakon wani tattaki da shi Muhammed Bello ya shirya don nuna adawa da abin da suka kira "yin ba daidai ba " .Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://www.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN