Guban hayakin janareto ya halaka iyalin mutum 6 | isyaku.com

Ana kyautata zaton cewa hayakin injin banwutan lantarki janareto yayi sanadin mutuwar wani magidanci da matarsa da kuma 'yayan sa su hudu 'yan shekara 6,4,3,da 2 a karamar hukumar Obio/Akpo da ke jihar Rivers.

Kakain hukumar 'yansanda na jihar Rivers Nnamdi Omoni ya shaida wa manema labarai haka.

Makwabta sun lura da abinda ke faruwa ne bayan sun fara jin wari yana busowa daga gidan mamatan wanda ake tunanin cewa lamarin ya farune tun ranar Juma'a da dare.

Bayanai sun nuna cewa an sami gawakin iyalin ne a palo na gidan da suke haya a mace wanda ake zaton cewa suna kallon talabijin ne barci ya kwashe su kafin hayakin janareton ya halaka su.

Hukumar 'yansanda na jihar Rivers ta kwashe gawakin inda take ci gaba da bincike akan lamarinKu biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN