Asibitin Sir Yahaya inda mara lafiya kan jira fiye da awa 7 kafin ya gan Likita

Duk da fitowa da wasu tsare tsare da mahukuntar Asibitin tunawa da Sarki Sir Yahaya a garin Birnin kebbi sukayi,wanda kuma Asibitin shine babban Asibiti mafi girma a fadin jihar Kebbi wanda ya fi dadewa kuma mafi samun cinkoson jama'a marasa lafiya amma bisa ga dukkan alamu da sauran aiki wajen ganin an wadatar da samar da jinya ko kulawar Likita ga mara lafiya a cikin lokaci ba tare da matsi daga bangarorin guda biyu ba,bangaren Likitoci da bangaren marasa lafiya musamman wadanda ke zuwa domin ganin Likitoci a bangaren je-ka -dawo ko OPD.

A 'yan watannin baya har zuwa yanzu,akwai zarge zargen cewa mahukuntar Asibitin sun tsananta dokoki  da yawa misali shigowa Asibitin domin awon hawan jini a sashen kulawa na gaggawa A&E wai sai dai maralafiya ya jira sai washe gari yaje OPD domin ya bi layi don ganin Likita kawai domin yana son a auna jininsa koda ya hau ko ya sauka ga masu lalurar hawan jini.

Haka kuma wai idan da mai hawan jini zai sami bijirewan magani kuma jinisa ya hau ko ya sauka a ranar Juma'a da karfe 6 na yamma saidai ya jira sai ranar Litinin kafin ya je Asibitin sashen OPD domin a duba shi watau jinin yana nan yana jira har sai ranar Litinin daga ranar Juma'a.

Bincike da muka yi ya tabbatar da cewa wannan tsari tuni yayi mumunnar tasiri a cikin al'umma musamman ga masu hawan jini da basu da na'urar auna jinin haka zalika lamarin ya shafi wadanda ke da ciwon suga wanda yakan taso daga lokaci zuwa lokaci da yake bukatar a auna domin a gan yawan suga a jiki.

Malam Sani wani mazauni unguwar bayan kara ne a garin Birnin kebbi ya shaida mana cewa shi yana da lalurar ciwon suga kuma baya da na'urar aunawa suga a jikinsa,"wani lokaci nikan ji cewa suga yayi karanci a jikina sai ma na sha suga kadan ,haka kuma wani lokaci sai inji kamar sugan yayi yawa wanda zaisa ala tilas in sha magani,ka gan ina bukatar a dinga aunani lokaci zuwa lokaci saboda lalurace da take tasowa ba wai tana da takamammen lokaci bane kafin ta taso"

Ganin cewa Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Alh.Atiku Bagudu tana iyakar kokarinta wajen bayar da tallafi,taimako da kayakin da suka wajaba domin inganta lafiya da kiwon lafiya a jihar Kebbi,amma yawancin lokaci akan gamu da rashin wadataccen tasiri wanda yakan samo asali  daga tsarin tafiyar da shiriin.

Akwai kuma zargin cewa wasu lokutan marashi lafiya yakan kai awa bakwai ko fiye kafin ya gan Likita a Asibitin Sir Yahaya a garin Birnin kebbi,wannan mun tabbatar da haka yayin da muka shiga Asibitin tun karfe 7:30 muka bi layi domin mu gan Likita amma har karfe 2:30 layi bai kai ta kanmu ba.

Wani abin ban haushi shine yadda aka kira wasu wadanda muka rigasu  shigowa kan layin ganin Likita amma sai aka kira su cikin dan kankanin lokaci yayin da sauran marasa lafiya ke kallo kiri-kiri.

Wani mara lafiya da baya son a ambaci suansa ya shaida mana cewa shi ya zo ne daga wani kauye da ke nan kusa da Birnin kebbi amma ya shiga layi domin ya gan Likita tun karfe 7:10 am amma ba'a kira shi ba sai karfe 2:18 pm alhali ya gan wanda yazo da karfe 12 pm amma zuwa 1:00 pm an kira shi ya gan Likita kuma ya tafi ya barsu a kan layi.

Bincike da muka yi akan lamarin ya nuna cewa rashin wadatattun Likitoci da masu taimaka masu wajen jinyar marasa lafiya Nas (Nurse) yayi tasiri wajen samun irin wadannan matsalolin da korafe korafe da hakan ya haifar.

Kokarin da muka yi domin mu ji  ta bakin mahukuntar Asibitin ya ci tura izuwa lokacin da muka wallafa wannan labarin.



 
Ku biyo mu a
https://www.facebook.com/isyakuweb
Don samun labaranmu ta Whatsapp ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye.
Don aiko Labari ko korafi ka tuntube mu a 08062543120.
Shiga www.isyaku.com Don samun cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN