Tuna baya: "Ba abinda ke cin dan Siyasa da wuri kamar yin karya" - Hon. Yakubu Rilisco

Shugabanci wani abu ne mai daraja da mutum ke nema da kansa ko kuma a bashi a bisa wasu dalilai ko na gargajiya,gado,addini ko ilimi akan fahimta.

A yau ISYAKU.COM ya tuntubi Dan Majalisa a Majalisar Dokoki na jihar Kebbi Hon.Bar Muhammed Bello Yakubu Rilisco akan ko yaya yake ganin Siyasa da yadda ya kamata a tafiyar da tsarin Siyasa.

"Hon Rilisco ya shaida mana cewa da farko dai Siyasa ba fitina bane ra'ayi ne kuma kowa zai iya yin abinda yaso ta hanyar zaben wanda yake so.Yadda kake da naka ra'ayi haka wani yana da nashi ra'ayi.Saboda haka mataki na farko shine a mutunta juna.

Yin zabe ta hanyar fitowa a kada kuri'a wata damace da mutum ke da ita domin rashin fitowa a yi zabe ya zama cutar da kai da kuma cutar da al'umma don rashin kada kuri'ar ka zai iya sa wanda bai cancanta ya ci zabe ba yazo yaci zaben kuma daga baya jama'a su dinga kuka akai.

Wadanda aka zaba kuma su sani ba wai mutum an zabe shi ne yazo yayi iko ba,yazo ne yayi wa mutane aiki.Ya kamata ya dauki kanshi kamar shine bawan jama'a ba wai maigidan jama'a ba saboda su ne suka taru suka jefa maka kuri'a ka kai kan kujera da matsayin da kake.

Haka ya isa ka sani cewa ba za ka iya kaiwa kan matsayi ko kujerar da kake ba sai jama'a sun kaika ta hanyar zabe.Idan ka kai kan kujerar sai ka kalli mutane da mutunci da idon rahama,abin da zai yiwu da gaske kayi masu,idan jama'a sunzo wajen ka ka saurare su.Abinda za ka iya yi ka yi ,kada kayi karya.Domin ba abinda ke cin dan Siyasa da wuri kamar yin karya,ko yin alkawarin karya.Saboda haka ka bi gaskiyar ka wannan itace maganar gaskiya."


Daga Isyaku Garba - Birnin kebbi
Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN