An tattauna don inganta tsaro a karamar hukumar Shanga | isyaku.com

Kantoman riko na karamar hukumar mulki ta shanga , Alh.Garba Salisu Takware ya zauna da dukkannin 'yan takara na karamar hukumar shanga tareda DPO da tawagarsa da kuma  SSS da sauran manya Shugabannin jam'iyar APC na Shanga .

An tattauna kan abubuwa masu muhimmanci musamman wa'yanda suka shafi harkar tsaro .A jawabin da shi DPO Yayi ya ja hankalin 'yan siyasa da cewa ,su tabbatar sun dauki matakin gudanarda yakin neman zabensu a cikin lumana da aminci , ba tare da tsokano wata rigimaba.

Haka shima DCO yayi fashin baki akan jawaban DPO , Inda yake cewa duk wani "Lafazi"da ake tunanin zai iya kawo rigima/tashin-hankali to ayi kokari a kaucemasa domin samun zaman lafiya a wannan karamar hukuma . Wannan jawabin yayi matukar daukar hankalin 'yan siyasa kwarai da gaske.

Daga karshe shugaban jam'iyar APC Alh. Bala Karhe 'yar-bashe ya tabbatar wa DPO cewa zasu yi iya na su kokari domin ganin cewa an gudanar da wannan yakin neman zaben cikin aminci da kwanciyar hankali


Sani Musa Saminaka daga Shanga.
Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120. Shiga shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN