• Labaran yau

  Zargi: "Ana nuna wariya tsakanin daliban Makarantar 'yansanda a Wudil" | isyaku.com

  Kungiyar Matasa Musulmai ta kasa da ake kira MYSC ta zargi hukumar Makarantar koyar da hafsoshin 'yansanda da ke Wudil a jihar Kano da keta haddin dalibai Musulmai wadanda ake horarwa a Makarantar wanda ake hana su zuwa ganin gida saboda  su yi bikin Sallah tare da iyalansu tun 2013.

  Daily Trust ta ruwaito cewa  a wani jawabi shugaban kungiyar Nasir Ahmad ya yi nuni da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya haramta banbanci tsakanin addinai ko al'umma.

  Nasir ya kara da cewa a yayin da ake hana Musulmai zuwa gida saboda bukukuwan Sallah su kuma takwarorin su Kiristoci akan barsu kowace Disamba su je hutu harma su yi shagulgulan Kirsimeti da iyalansu.

  A ci gaba da bayaninsa akan lamarin Mal.Nasir ya kara da cewa sau da yawa hukumomin makarantar ke sanya lokacin jarabawa a ranakun Juma'a wanda hakan yakan hana Musulmai samun sukuni su je Sallar Juma'a.

  Daga karshe Nasir Ahmad ya roki babban safeto janar na 'yansandan Najeriya Ibrahim Kpotun Idris akan ya duba lamarin da idon basira saboda ya taimaka a kawo daidato a tsakanin daliban Makarantar domin a tabbatar da adalci.
  @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.
  • Facebook Comments

  0 comments:

  Post a Comment

  Rubuta ra ayin ka

  Item Reviewed: Zargi: "Ana nuna wariya tsakanin daliban Makarantar 'yansanda a Wudil" | isyaku.com Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama