Mafi tsawon rai a Duniya: Tsohuwa mai shekara 131 | isyaku.com

Wata tsohuwa mai suna Alimiha da ake kyautata zaton cewa ita ce mace mafi tsufa a Duniya ta ce an haife ta ne a watan Yuni 15,1886 a kasar China.Tsohuwar dai tana murnar cikanta shekara 131 tare da jininta mutum 56 wanda ta haifa su ma suna tare da ita a wajen bikin.

A cewar kamfanin labarai na China,duk da tsufar wannan tsohuwar wani Likita Abdul Rusuli ya binciki matar inda ya samu cewa suga da jinin ta daidai suke,ma'ana babu ciwon suga ko hawan jini a tare da ita.

Hukumar kididdigar adadin mace-mace da rayuwa na China ta bayyana Alimiha a matsayin wadda ta fi kowa tsawon rayuwa a Duniya.

Amma Guinnes World Records ta fito da wani jawabi inda ta ce wata mace mai suna Jeanne Calment 'yar kasar Faransa ita ce wanda ta fi  kowa dadewa a Duniya.An haifi Jeanne 1875 kuma ta mutu a 1997 kenan tana da shekara 122 da kwanaki 164 a Duniya kafin mutuwarta. 
Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120.DOWNLOAD OUR APPLICATION.APK 

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN