Kwankwaso: "Filayen da Igbo suka mallaka a Arewa yafi girman gabadayan yankin kudu a Najeriya"

Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yace 'yan kalibar Inyamirai da aka fi sani da Igbo ba zasu iya barin kasar Arewa ba sakamakon dimbin dukiya da suka mallaka a kasar Arewa.

Kwankwaso ya ce girman filaye da Igbo suka mallaka a kasar Arewa idan aka hadasu gaba daya yafi girman yankinsu na Inyamirai a Najeriya gaba daya.

A yayin da yake amsa tambaya dangane da rigingimu da suke tasowa game da wasu Igbo da ke neman kafa kasar Biafra ta Igbo zalla,da kuma wasu Matasan Arewa da ke bayar da wa'adi kan cewa Igbo su fice daga yankin Arewa,Kwankwaso yace" Babu wani dan kabilar Igbo mazauni Arewa da zai goyi bayan cewa ya koma kasar Biafra ko kuma Najeriya ta rabu gida biyu"

Kwankwaso ya ci gaba da cewa" Wajibi ne dukkannin wadanda lamarin ya shafa su fito da tsari na gaggawa domin a tabbatar da zaman lafiya da mutunta juna,ya kuma yi mamakin ganin cewa bayan Nnamdi Kanu ya tayar da hankalin mutane kuma ya wulakanta jama'a sai gashi ana karadin cewa zai fito ya tsaya takara a zabe"


@isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a SMS zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN