Kishi mugun ciwo: Yadda ta kasance da wasu kishiyoyi a garin Saminaka a Shanga L.govt | isyaku.com

Kamar yadda muka bada labarin kishiyoyi da abinda ke gudana a tsakaninsu a jiya  Talata , domin kara Jin yadda asalin lamarin yake da kuma inda aka kwana ayanzuhaka , na dauki dogon lokaci ina zantawa da mijin wa'yannan matan(mai suna  Malam Adamu Amin-malan)a garin Saminaka dake karamar hukumar mulki ta shanga .

Na nemi cikakken bayani gameda wannan Lamarin ga shi Malam Adamu Amin-malan , yace mini wannan lamarin dai yayi matukar bashi tsoro a irin yanayinda yaga matarsa wadda ake tuhumar ansawa guba cikin abin shanta mai suna Hafsatu(wadda akasawa guba kenan)! Yace bayan sunje wurin 'yansada sai aka fahimci akwai kissa cikin wannan lamarin na Hafsatu , sabodahaka kai tsaye akaje da ita asibiti(G.H SHANGA) likita ya tabbatar cewa babu guba ko kadan ajikin wannan matan ! To fah ! Sai hankalin uwar gida yafara dawowa ajikinta wato Hajara(wacce ake zargin ta sanyawa dayan guba) .

Wannan ne yasa shi kanshi mijin hankalinsa ya dawo ajikin shi , bayanda can yana cikin matukar damuwa.Wannan ya kara sanardashi wani sabon darasi(acewarsa) domin yakara fahimtar cewa ita Hafsatu itace mai tsanin kishi sama ga Hajara saboda haka tayi amfani da wannan hanya/salo domin cimma manufarta gameda abukiyar zama . Likita ya ya tambayeta gameda yanayinda takeji ajikinta kafin ya gudanarda awo akanta. Sai ta nuna mai cewa Tasha gubane ! Nantake likita ya yi nashi aiki ya kuma tabbatar da cewa wannan ba gaskiya bane .

Idan dai akwai wani abu tsakaninku shikenan amma maganar guba ba gaskiya bane. Abinda zaibaka mamaki anan shine ita wannan amaryan wato Hafsatu gata dauke da kwano mai guba aciki da sunan cewa Hajara ce ta sanya guba domin ta halakar da ita. (A nawa dogon Nazari da nayi sai Nagano cewa ita Hafsatu iatace ta sanyawa kanta guba amma taki tasha sai tayi ha'inci ta ce 'yar'uwartace ta sanya wannan guba domin ta cimma manufarta).

 Ahalin yanzu dai dukkanin matan suna gidan mijinsu(Malam Adamu Amin-malan). Saidai Malam Adamu Amin-malan ya nuna mini fargabarsa sosai saboda umurnin da aka basu daga ofishin 'yansada na komawa "charge office" ranar Attanin maizuwa ko meye zai faru a ranar bai saniba . Wato mugunta irinta kishi aji-ajice , ko wace da nata salo . Ya Allah ka yimuna tsari da mugun kishi.


Daga S.M Saminaka.


Ku biyo mu a shafin mu na Facebook @isyakuweb https://web.facebook.com/isyakuweb Kana sha'awar ka sami labaranmu ta Whatsapp ? ka rubuto YES a Whatsapp zuwa 08062543120 zamu aiko maka da Labaran mu kai tsaye kyauta a koda yaushe muka wallafa Labari. Kana da sha'awar taimaka mana da Labarai, ko sharhi ? ka kira mu a 08062543120.
Shiga babban shafinmu kai tsaye domin samun cikakkun Labarai.Ka shiga www.isyaku.com a browser ko opera ko firefox ko safari na wayarka zaka sami cikakken shafinmu da ke dauke da ababe masu kayatarwa.

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN